15 Mayu 2014 - 11:17

Wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kan kauyen Alau Ngawo fate da ke jihar Borno, inda suka kona daukacin kauyen.

Mutum biyu sun mutu a harin da 'yan bindigar suka kai kan kauyen dake karamar hukumar Jere, a ranar Laraba da daddare.

Haka kuma rahotanni daga garin Gamboru Ngala na cewa tun da safiyar ranar Alhamis ne mazauna garin ke jin harbe-harben bindiga.

Kimanin mutane fiye da 300 'yan bindiga suka kashe tare da kona kasuwar garin a 'yan kwanakin da suka wuce.ABNA.